الأحد، فبراير 10، 2008

majalisar dinkin duniya

sudanesehawsa.com


Muhimmin Jawabin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana game da Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948 Gabatarwa Ganin cewa yanci da adalci da zaman lafiya ba za su girku a duniya ba, sai in an amince da cewa: dukkan yan-adam suna da mutunci, kuma suna da hakkoki na kowa daidai da na kowa, wadanda ba za a iya kwace musu ba, Ganin cewa ba abin da ya sa aka aikata abubuwa irin na lokacin jahiliyya wadanda ke tada hankalin duniya gaba-daya, illa rashin sanin hakkokin dan-adam da rena su. Ganin kuma cewa an bayyana cewa: muhimmin gurin da yan-adam suka sa gaba shi ne, bayan sun kubuta daga tsananin iko da wahala, kowa ya sami damar fadin ra''ayinsa kuma ya sa rai ga abin da zuciyarsa ta saka masa, Ganin cewa ya kamata a kafa hukumomi wadanda za su kula da kiyayewa da hakkokin yan-adam, ta hanyar girka dokoki, domin kada tsananin iko da danniya su yi yawa har su kai mutane ga yin kara ko yin tawaye, Ganin cewa ya kamata a karfafa aminci tsakanin kasashe, Ganin cewa a cikin usular (takardar sharuda) al''ummu, kasashen duniya sun sake nuna amincewarsu da muhimman hakkokin yan-adam, da mutuncinsu, da darajar da wadannan halittu suke da ita kuma a kan daidai-wa-daida ga namiji da mace, suka kuma dauki alkawalin yin kokari domin su kyautata wa yan-adam jin dadin rayuwa a cikin suna kara walawa da