الاثنين، يناير 26، 2009

hausa grammer


dansudan

Hausa marks verb tenses with different sets of subject pronouns rather than marking changes in the verbs themselves. There are therefore separate sets of subject pronouns for all the Hausa verb tenses. Examples here illustrate the third person singular subject pronoun for each "tense". Click the highlighted links to see the full pronoun paradigms

Completive
Sun sha shayi. ________________'They drank tea

Relative Completive
Shayi suka sha. ____________'It tea that they drank

Negative Completive
Ba su sha shayi ba. __________ 'They didn't drink tea

Continuative
Suna shan shayi. ___________ 'They are drinking tea
Relative Continuative
Shayi suke sha. _______'It is tea that they are drinking

Negative Continuative I
Ba sa shan shayi. ___________'They aren't drinking tea
Negative Continuative II
Ba su da mota. ______________'They don't have a car
Future
Za su sha shayi. _______________'They will drink tea

Subjunctive
Su sha shayi. _______________'They should drink tea

"Indefinite" Future
Sa sha shayi. ____________'They will surely drank tea
Habitual
Sukan sha shayi. _________________'They drink tea

الأربعاء، يناير 21، 2009

Tarihin Barack Obama

An aifi Barack Hussain Obama ranar 4 ga watan Oguster na shekara ta 1961 a birnin n Honolulu dake yankin Hawai a ƙasar Amurika.
Tun yana ɗan shekaru biyu da aihuwa iyayensa suka rabu, ya cigaba da zama tare da ma´aifiyarsa.
Ubansa musulmi ƙan kasar Kenya a nahiyar Afrika, ya bar Amurika bayan ya rabu da matarsa ba´amurika inda ya koma gida Kenya, ya kuma zama minister a cikin gwamnatin shugaban ƙasa na farko, wato Jomo Keniyatta, kamin Allah ya amshi ransa, a shekara ta 1982 a cikin haɗarin mota.
A lokacin da ya samu shekaru shida, har zuwa shekaru 10, Barack Obama ya bi ma´aifiyarsa a ƙasar Indonesia inda suka yi zama na shekaru huɗu.
Sai a shekara ta 1971 ya komo Honolulu, inda ya ci gaba da karatu.
Yayi karatu a jami´ar Californiya da kuma ta Columbiya a birnin New York.
Bayan ya kamalla karatu, a jami´a, Obama ya fara aiki a matsayin jami´i, ta fannin lissafin kudi.
To saidai ba jima ba yana wannan aiki ya kuma koma ƙarin ilimi, inda a shekara ta 1991 ya fito da digrin digirgir ta fannin sharia´a.
Barack ya jima ya na kwaɗayin shida siyasa, amma sai a shekara ta 1996 haƙƙarsa ta cimma ruwa, inda karon farko a ka zaɓe shi a matsayin dan majalisar a mazaɓarsa ta yankin Ilinois.
A shekara ta 2004 ya shiga Majalisar Dokokin Amurika.
A tsawan watani 18 Barack Obama na fafatawa da matar tsofan shugaban ƙasar Amurika, wato Hilary Clinton domin samun tabaraki daga jam´iyar Demokrate don tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurikar.
A wani matakin da wasu ke dangatawa da "rabbo rabbabe", babbu zato babu tammaha, Barack Obama ya kai gaci tare da kasa abikiyar hammayar tasa.
A duk tsawan wannan lokaci Obama ya bayyana kansa a matsayin gwarzo, duk da cewar da dama na masa zargin rashin ƙurrewa cikin harakokin siyasa, idan aka kwatanta shi da Hilary Clinton, ko kuma da ɗan takara jam´iyar Republicain John Makain, mai shekaru 72 a duniya,wanda kuma ya laƙanci ƙabli da ba´adin siyasa, a ciki da wajen Amurika.
Ta fannin rubuce rubuce,Barack Obama, ya rubuta littatafai guda biyu, inda a ɗaya daga cikin su, yayi tarihin rayuwar baƙƙaƙe a Amurika, tare da bayyana yadda a matsayinsa na baƙin ba´amurike ya gudanar da yarintarsa.
Barack Obama,na da aure da kuma ´yaya,´yan mata guda biyu.


.

الثلاثاء، يناير 20، 2009

Bush Yayi Ban Kwana Da Washington


dansudan

Shugaba George W. Bush yayi ban kwana da fadar White House a matsayinsa na Shugaban Amurka.
Mr Bush da uwargidansa Laura sun halarci wajen rantsar da Shugaba Barack Obama, wanda ya gaje shi.
Tun da safe saida Mr. Bush da uwargida Laura, suka karbi Shugaba Barack Obama da uwargida Michelle a fadar White House, inda suka yi karin kumallo tare, daga inda suka wuce harabar Majalisar Dokoki kai tsaye domin bikin kaddamarwar.
Mr. Bush ya bar ofis da mafi karancin tagomashi da wani Shugaban Kasa mai barin gado ya taba fuskanta a tarihin siyasar Amurka.
Bayan kammala bukukuwan rantsuwar, iyalin na Bush sun shiga jirgi mai saukar ungulu, zuwa filin jiragen saman Dakarun saman Amurka na Andrews, dake nan bayan garin Washington, inda za a yi masa bukukuwan ban kwanan kafin ya tashi zuwa Texas.
Kafin ya bar ofis, saida tsohon Shugaba Bush ya barwa Shugaba Obama wata takarda kan teburinsa dake ofishin shugaban kasa. Kakakin Shugaba Bush Dana Perino tace Mr. Bush ya bar takardar a cikin aljihun teburin a jiya da dare. Saidai bata yi bayanin abin da takardar ta kunsa ba.
Mr. Bush zai halarci wani bikin yi masa maraba da dawowa gida a kauyensu na Midland, Jihar Texas, kafin ya zarce zuwa gidan gonarsa dake Crowford. Daga karshe dai Bush da uwargidansa zasu koma Dallas, bayan kammala 'yan gyare-gyare.

الاثنين، يناير 19، 2009

Shirye Shiryen Rantsar Da Obama









dansudan
Ana ci gaba da bukuwan share fagen rantsar da Shugaban Amurka na 44, kuma bakar fata na Farko a gobe talata 20 ga 01 - 2009 . An tsaurara tsaro, kuma ana ci gaba da kawata harabar Majalisar Amurka
.A yau Litinin Shugaban Amurka mai jiran gado, Barack Obama ya yabi mai
fafutukar kwatar 'yancin dan adam dinnan na Amurka, Martin Luther King Junior, saboda Yau fifikon da ya bayar kan aikin jama'a.yau ranar hutu ce a Amurka wadda aka ware domin
A jiya Lahadi ma, Obama ya halarci bukukuwan share fagen kaddamar da shi a matsayin Shugaban Kasa na 44, inda ya kai ziyara zuwa makabartar soji domin karrama sojojin da suka karrama Martin Luther King, wadda kuma ake amfanim da ita wajen karfafa guiwar aikin gayya. A jiya Lahadi ma
wa'yannan shugabanin Amurka ne daga na farko zowa Obama


رؤساء الولايات المتحدة
1- 1789 : جورج واشنطن2- 1797 : جون آدامز3- 1801 : توماس جفرسون4- 1809 : جيمس ماديسون5- 1817 : جيمس مونرو6- 1825 : جون كوينسي آدامز7- 1829 : أندرو جاكسون8- 1837 : مارتن فان بيورين9- 1841 : ويليام هنري هاريسون
10- 1841 : جون تايلر11- 1845 : جيمس بولك12- 1849 : زكاري تايلور13- 1850 : ميلارد فيلمور14- 1853 : فرانكلين بيرس15- 1857 : جيمس بيوكانان16- 1861 : أبراهام لينكون17- 1865 : أندرو جونسون18- 1869 : يوليسيس جرانت
19- 1877 : رذرفورد هايز20- 1881 : جيمس جارفيلد21- 1881 : تشستر آرثر22- 1885 : جروفر كليفلاند23- 1889 : بنجامين هاريسون24- 1893 : جروفر كليفلاند25- 1897 : ويليام مكينلي26- 1901 : ثيودور روزفلت27- 1909 : ويليام هوارد تافت
28- 1913 : وودرو ويلسون29- 1921 : وارن هاردنج30- 1923 : كالفين كوليدج31- 1929 : هربرت هوفر32- 1933 : فرانكلين روزفلت33- 1945 : هاري ترومان34- 1953 : دوايت أيزنهاور35- 1961 : جون كندي36- 1963 : ليندون جونسون
37- 1969 : ريتشارد نيكسون38- 1974 : جيرالد فورد39- 1977 : جيمي كارتر40- 1981 : رونالد ريغان41- 1989 : جورج بوش الأب42- 1993 : بيل كلينتون43- 2001 : جورج دبليو بوش44- 2009 : باراك أوباما