الأحد، فبراير 21، 2010

Sojoji Sun Hambarar Da Mamadou Tandja Daga Kan Mulki

Mamadou Tanjda
a rana 18 ga wata na 2 a shekara ta 2010 Sojoji a Jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar kafa sabuwar Babbar Majalisar Maido da Dimokuradiyya, a bayan da suka hambarar da gwamnatin shugaba Mamadou Tandja.

A cikin wata sanarwar da kakakin sabuwar majalisar da ake kira "CSRD" a takaice cikin harshen Faransanci, Kanar Abdoulkarim Goukoye, ya bayar ga 'yan jarida, yace an dakatar da yin aiki da tsarin mulki, yayin da aka rushe dukkan cibiyoyin da aka kafa karkashin tsarin mulkin.


Sojojin sun yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, su na masu fadin cewa ba su yi juyin mulkin domin kuntatawa wani ko wasu ba.


Sabbin hukumomin kasar ta Nijar sun bayyana kafa dokar hana fita waje daga karfe shida na maraice zuwa shida na safe.


Babu wani karin hasken da kakakin na sojoji ya bayar a game da halin da Mamadou Tandja yake ciki, haka kuma babu wani bayani game da ministocinsa da aka ce an kama su.

الجمعة، فبراير 05، 2010

Tarayyar Afirka Zata Ladabtar Da Duk Wadanda Suka Shirya Juyin Mulkin Soja Cikin Ko Wace Kasa A Nahiyar

An kammala taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka jiya a Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia.

A jawabin rufe taron, sabon shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Malawi, Bingu wa Mutharika, ya dauki alkawarin yin aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afirka tare da kokarta hana juyin mulkin soja, san nan ya kara da cewa wajibi ne a dauki matakin ayyana yaki gadan-gadan a kan sauya gwamnati ba bisa tsarin mulkin kasa ba a nahiyar Afirka, yace "mun kuma zartas da cewa za’a dauki matakin ladabtarwa mai karfi a kan duk wanda yayi jagorancin juyin mulki da wadanda suka taimaka wajen samar da kwarin gwiwar gudanar da juyin mulkin"

.Shi kuwa kwamishinan harkokin tsaro da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka Ramtane Lamamra cewa yayi, kungiyar Tarayyar Afirka mai kasashe 53 dake da wakilci cikinta sun amince da kudurin daukan matakan hana juyin mulki a Afirka amma ba’a bayyana irin matakan da za’a dauka ba.

Kasashen Mauritania, da Guinea da Madagascar sun hadu da juyin mulkin soja cikin watanni goma sha takwas da suka gabata.