SHARHIN LITTAFI
ALKAWARIN FANSA
Sunan Mawallafiya: Aishatu Haruna Abubakar
Suna Littafi: Alkawarin Fansa
Yawan Shafi: Saba'in (70)
Farashin Littafi: Naira Arba'in (N40)
Shaekarar Bugu: Babu, kaico!
Kamfanin Dab'i: Mureeh Printing Pess
Manufar Yin Nazari: Bunkasa Adabin Hausa
Marubuci/Manazarci: Almustapha Adam Muhd.
Kwanan Wata: 13/1/2008
TSIFA
Alkawarin Fansa labari ne da yake kunshe da ramuwar gayya ko in ce alkawarin daukar fansa kamar yadda Marubuciyar ta radawa littafin suna. Hakika littafin ya amsa sunansa, na fahimci hakan saboda yadda Abubakar ya jure, ya turje, ya dake, ya share, ya nunawa duniya sam cin mutuncin da Halima (Hali Hot) ta yi masa bai damu ba, har Allah ya nufa ya aure ta.
A bangare daya kuma littafin ya amsa sunan shirme da shirirta, har da soki-burutsu da baragada.
Tun farko bangon littafin ya bayyana da hoton wata budurwa kanta babu kallabi, kuma sanye a jikinta wata matsattsiyar riga ce da ta bayyanar da qirjinta a fili, kowa yana gani. Hannayenta ma haka. Ya kasance abin takaici, ga duk wanda ya fahimci littafin na bahaushiya ne kuma an rubuta da Hausa saboda dalilan da mafi yawan marubuta suka dogara da su na yin rubutunsu. Bunkasa harshe, adabi, da kuma al'adun Hausa su ne mafi girman dalilan nasu. Amma abin mamaki hoton bangon littafin ya gaza wakiltar kabilar Hausawa, ko ku kun yarda wannan shiga kabilar Hausawa ce? Kuma dan Allah ya za ku ji idan duniya ta nuna wannan shiga a matsayin Hausawa?
Haka kuma bangon littafin bai wakilci musulinci ba, kaico!
Na san zai kasance abin takaicci da baqin ciki ga 'yan uwa musulm idan aka ce wannan shiga ta musulmi ce, ko ba haka ba?
Musulinci ya nuna mana shigar da ya dace maza da mata, domin jikin mace al'aura ce idan ka cire tafukan hannayenta da fuskarta. Allah ka yi masa katangar karfe da duk rubutun da ba zai nuna mana yadda za mu ci gaba da inganta addininmu na musulinci ba da al'adunmu na Hausawa ba.
Wani cikakken nazari da na kara yi wa wannan littafi, na gane ba ya dauke da sakon alheri sai na batsa da yadda ake soyayyar zamani.
Misali a shafi na biyu sakin layi na 3, marubuciyar ta rubuta ''............ sai jin nononsa ya yi a bakinta tana tsotsa. A shafi na 3 ta rubuta ''.......... .ya ciro hannunsa daga qirjinsa ya yi nuni da yatsansa izuwa kasan mararsa..... . A shafi na 20 sakin layi na 3 ta rubuta ''.......... ..har ka mutu ba ka isa ka san wandona ba, balle mafitsarata, wannan gun da ka gani (ta yi nuni izuwa kasan mararta) kai da shi har abada ba naka ba ne, ba na masu karamar halitta ba ne irin ka.''
A shafin dai sidira ta 6 ta rubuta ''..........don ko a mafarki ka yi mafarkin ka aure ni, ka hau wannan ruwan cikin nawa ban yafe maka ba.'' A shafi na 21 sakin layi na 2 ta ce ''.....Oh yes, kowanne xan iska idan ya ji abu na reto a kasan mararsa sai ya kira kansa namiji.....' ' ta nuna tsakiyar cinyarsa da yatsa.
A shafi na 23 layi na 3 ta ce ''......ya tallafo ta jikinsa ya sa hannayensa biyu ya dago kanta'' A shafin dai sakin layi na 4 ta ce ''.....ya riko ta a dai dai lokacin da yake dadumar fuskarta da tashi, kan ta kai ga fuskantar abin da yake nufi, har Tahir ya jefa bakinsa a nata ya sakar mata wani dan karamin kis mai kara. Tir! da wadannan fitsararrun munan kalamu da ke cikin littafin Alkawarin Fansa, kusan duk shafukan littafin haka suke dauke da zunzurutun tsagwaran tsantsar tsabagen batsa sanho-sanho.
A shafi na 60 sidira ta 2 ta ce ''.....in ban da rungume-rungume da tsotse-tsotsen juna ba abin da suke yi. A shafi na 63 sakin layi na 2 sidira ta 4 ta ce, ''.......kallonta izuwa kasa da cibiyarsa ta ga lallai in ba a kai masa agajin gaggawa ba, zai iya tashin gajeren wandonsa daga aiki.
A shafi na 63 dai marubuciyar ta ce ''......tun daga nan ya fara zare mata kaya yana wulli da su har sai da ya sulle ta tas, sannan suka kicime da lalube juna kamar wadanda suka shekara suna kishirwar kansu. Da kyar suka kai junan su daki suka wara kokarinsu suka yi ta jan jarabarsu... .'' Amma dai tur da wannan batsa muraran, karin mamaki marubuciyar dai bata baiwa taurarin umarnin yin addu'o'in da Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W) Ya yi umarni da a yi a daren farko ba kuma wai auren sunnah. Amma dai kaico!
A shafi na 67 sakin layi na 3 sidira ta 5 ta ce, '........... ..ni din nan ban isa in ga inda kike yin fitsari ba balle kallon wandonki, na hau wannan ruwan cikin naki da ka kika ce ya yi min nisa in yi sukuwa.''
Kai ka ji, ni kam na yi matukar mamaki a wannan marubuciya haka kawai ta batawa kanta lokaci ta rubuta littaf mai doyi marar ma'ana mai cike da batsa kamar wani abin kirki ta yi, ka gara ma ta sa wa littafin suna Bats a da dangoginta ko Fitsara a sarari.
Wani karin rashin tabbatacciyar manufa na wannan lit tafi shine, yadda marubuciyar a shafi na 40 saki layi na 3 sidira ta 2 ta nuna wa duniya shimfidun alfarma da maka-makan kujeru su za ka gani ka gamsu da cewa gidan manyan mutane ka shiga.
Ni na kalubalance ta akan wannan, domin duk gidan manyan mutane za ka same shi cike da tarbiya, mutunci, da karamci. Ba kuma za ka sami 'yar manyan mutane da kawaye 'yan iska ba ballantana kuma ka ganta samari suna rage mata hanya a mota. Za ka sami 'yar manyan mutane da sanin ya kamata, domin tana da cikakkiyar tarbiya. Ba za ka sami 'yar manyan mutane tana biyewa saurayi har yana kakkama ta ba, ta kai har yana rungume ta ba.
Wani abu kuma da shi ma ya ja hankalina shi ne, yadda marubuciyar ta ce da makaranta, Abubakar ma ci amanar matar, cikakken dan bariki, mai almubazzaranci, mai taurin kai ga rashin hakuri wai halin Kanawa ne da shi, har wani ikrari yake shi cikakken Bakano ne, kuma so yake ya tabbatar da fadar nan ta ''Kano ko da me ka zo an fi ka.''
To albishirin ki, Kanawa sun sami wannan taken saboda yakana da karamci, ga tausayi da san bako amma ba da munanan halaye irin na Abubakar ba. Wannan ya faru ne a shafi na 58.
Haka Marubuciyar ta yi abin da ya yi mata dadi da taimakon ishasshen alkalaminta maras tsinkaye.
A nan kuma na cika da mamaki fal da marubuciyar ta kasa tabbatar wa da makaranta ita cikakkiyar Bahaushiya ce. Alal misali, a shafi na 4 sakin layi na 2 sidira ta 6 ta rubuta akwai a maimakon akai A shafi na 7 sakin layi na 4 idira ta 2 ta ce Bugur a maimakon Bugar A shafi na 14 sakin layi na sidira ta 6 ta rubuta junkuri a maimakon yunkuri. Kusan duk shafukan haka za ka yi ta cin karo da su.
Wannan karon kuma takaici ne ya turniqe ni saboda yadda na ga marubuciyar littafin Hausa ta sauya zuwa hamshakiyar baturiya, kaico!
A shafi na 41 sidira ta 7 ta ce pine apple juice.A shafi na 8 sakin layi na 1 sidira ta 5 ta kuma rubuta happeining girl abin mamaki kuma wannan kalaman sun fito daga bakin marubuciyar ba wai daga bakin taurarin labarin ba. Kai ina shakkar in har wannan littafin ya shiga hannuna masana.
Marubuciyar ba ta tsaya nan ba, sai da ta yi kokarin nunawa makaranta a na gina soyayya akan turbar karya, yaudara da kwadayi, sannan kuma ta rikide ta zama ta gaskiya a cikin dan kankanin lokaci. Anya kuwa haka na kasancewa?
''Kin san fa ba batun so muke yi ba, tun da Abubakar shi ne mai boza kin san agunsa nake.....'' To kun ji daga bakin Halima a shafi na 50, kun ga kenan don abin hannunsa take sona, in babu kuma gudunsa za ta yi, domin ba Allah a zuciyarta, saboda don kudi aka gina soyayyar.
''Karyar dai fure take ba ta 'ya'ya.''
Rashin kan gadon labarin ya daukaka ta kai labarin ya rasa kima da dara. Labarin babu gabatarwa, babu ma shekarar bugu da aka yi littafin. Turkashi! Wannan shi ne kwamacala. Da marubuciyar za ta gane da ta janye littafin daga kasuwa saboda ba shi da wata mamora don da ma muguwar rawa gwanda kin tashi. Rashin sa ya fi samar da shi amfani nesa ba kusa ba!
Da wannan nake neman afuwa a gun marubuciyar idan har wannan dan nazarin da na yi ya bata mata. Allah ya sa kuma ki fuskanci manufata.
Ni ne Makaranci/Marubuci/ Manazarci:
ALMUSTAPHA ADAM MUHAMMA
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق