السبت، يونيو 07، 2008

TARBIYAR TSIRAICI

dansudan
Sanannen abune cewa kasashe masu kaffa-kaffa daaddinin su da al'adunsu na kwarai suna kokarin maidafinafinai da wasan kwaikwayo wata kafa ta tattauna matsalaralumma da tarbiya da bada tunani na gari, sabanin halindamuke a kasar hausa na karkatar da wannan dama zuwagwada kwarewa wajen nuna rashin kunya da da koyawamanyan gobe munanan dabi'u daga baya kuma sai ace anakokarin gyara tarbiya to lallai bamu ba tarbiya har duniya tatashi indai yan daba da mata masu cin gashin kansu dawadanda aka kasa tarbiyarsu suka gudu suka bar tarbiya su-ne masu tarbiya kai abun dariya da takaici duk da hakashuwagabanni da wadanda abun ya shafa basu yi yunkurinhanawa ko kokarin garkatar da akalar fina-finan izuwa koyarda tarbiyar gaskiya ba . to yanzu abun yakai ga dole kowa yaciza yatsa , akwai matukar da takaici ace yar fim ta fito tsirarahar na tsawon dakikai takwas kan gado sannan wani yazo yahaukanta yayi tsiyar da zaiyi da ita, sannan yayi wani irinnau'i na wasa da maniyinsa kan cinyarta , kai ! wallahi ,na'uzu billahi minashshaidanirrajim! wani irin dabbanci kenan?kuma abun mamaki harda cewa '' a gafarcemu'' ammawannan yarinya taci sunanta ''HIYANA'' don kuwa ta ha'inciduk musulmin duniya, ta kuma tona asirin musulmin najeriya.
Duk wani mai zurfin tunani yasan hakan zata faru tundakokari suke su kwaikwayi [nigerian film] su kuwa wannan babako bane gunsu, ga wani abunda na taba karantawa jaridargaskiya tafi kwabo ''GTK: To, a matsayinki na wadda take fitowa a fina-finanHausa da na Turanci, yaya za ki kwatanta bambancin da ketsakanin fina-finanmu na Arewa da kuma na Kudanci?
HAUWA MAINA: Ai dai wannan ne ko kuma aka tambaya, zaku iya fadin bambancin (dariya).
GTK: Amma da yake ke kina cikin harkar ne, ina ganin ke yafi cancanta ki yi mana bayani.
HAUWA MAINA: To shi kenan, a gaskiya, ’yan Kudu sun yimana fintinkau in dai za a yi maganar gaskiya ce. AmmaAlhamdulillahi mu ma mun fara shiga sahunsu, saboda idanaka yi la’akari da irin na’urorin da suke amfani da su, to,yanzu mu ma mun fara samun irin wa]dannan na’urorin. Hakakuma ’yan wasanmu na Hausa su ma yanzu sun zaburo, sunakuma kokari sosai. Saboda haka nan ba da jimawa ba za murika hada kafada da kafada da su.''
Hakika abun daya ban mamaki cikin wannan al'amari babukamar wasu masu kokarin wanketa da cewa ai ba fim dintsiraici bane, saboda wannan wani abu ne tsakaninta dasaurayinta bai da alaka da fim, to amma ai ita jaruma ce awannan harka ta tarbiya, wa ya sani ko ta sadaukar da kantane wajen gyara al'adun banza har ta fara yada tarbiya kyautaana yada ta a blue tooth cikin kayan mutunci , domin ayi koyida ita, sannan an sakar muku haka ne , shin wannan bayagwada cewa wata ran za'a yi hakan a tsare da furodusa dadukkan shikashikai da sharuddan fim.
sannan wasu kuma sun bige da cewa taci mutuncin hausa-fulani ina ruwan wannan matsala da hausa fulani , wasu nacewa daman ba hausawa bane masu yi , hakika wannankarya ce mai girma da neman wanke kai na banza da wofi ,to kai in ma haka ne , waya basu izinin shigowa kano, jama'akar mu rudi kammu, hausa fulani dai a duniya zamu bar shiba wani abu mai anfani gun Allah sai musulunci.
IYAYE : sune kashin bayan tarbiyar 'ya'ya kuma sunematakin da idan yaro ya rasa ko sukai sakaci dashi rayuwarsazata shiga wani yanayi wanda bara aji dadin karshenta ba,wani yana cewa '' uwa makaranta ce idan ka shirya ta kamarka shirya al'umma ne'' kuma kamar yadda kowa ya saniwadannan masu cin abinci da lalata tarbiyar manyan gobegalibinsu in bamu ce duka ba sun fuskanci matsala da iyayekamar auren dole ko rashin mai riko mai kyau ko rashin tsawada kwaba don haka dole iyaye su dau hakurin daukan kasomai girma na laifi saboda kaso mai girman ba suke dashiwajen jibintan yayansu da kuma damar tarbiya.
YAN WASA: saboda sune masu fuskantar da wannanmatsala zuwa ga alumma kai tsaye don haka duk da barrantarda kan- su da wasu uzurori da suke bayarwa wanda zai yiwuya su kansu su yarda da su a cikin zukatansu balleal'umma gaba daya. Su dai kokarin su dole sai sun kwaikwayi turawa alhali kuwakowa yana kokarin bada gudumawane daidai al'ummarsa,idan bature da baturiya sukai wani rashin kunya a wasankwaikwayo to saiku duba cewa to shin kowa a cikin jama'arkuba rike ya ke da addini ba ? ba tare yake da mafadi ba? Shinburgewa a garemu shine mu fita daga shingen iyaye dasunan yanci? Wadannan banbance-banbance na addini daal'ada idan ba'a duba su ba to zamu jima cikin wannan rami,mu fito mun yi kura duk wanda ya kallemu ba zai iyamaimaitawa ba.
SHUGABANNI: wato duk Wanda yake da damar fada ajiamma bai hango matsalar da zata iya jawowa masuzuwa ba, ko ya hango baiyi kokarin kawo sauyi ba .
Daga karshe ina kara rokon wanda abun ya shafa da suyihattara wajen daidaita wannan wasa inda zaiyi daidai daaddinin jama'arsu da al'adunsu na kwarai , inba haka ba muyi batan bakatantan bamu ga namu bamu ga nasu .
Allah ya raba mu da sharrin shaidan.

ليست هناك تعليقات: