An gudanar da jana'izar shahararren mawakin nan Michael Jackson, wanda ya rasu bisa zargin an shayar da shi magunguna masu sa bacci fiye da kima a jihar Carlifornia ta Amurka.Mutane kimanin dari biyu da suka hada da 'yan uwa da abokan arziki suka halarci jana'izar da aka gudanar a makabartar Forest Lawn Glendale Park dake wajen birnin Los Angeles.
Sai dai an sanya kaida wajen halartar jana'izar ga manema labaru, sannan an umurci masoyansa da cewa kada kowa ya je.
Shugabannin sojin Amurka, wadanda suka hada da sakataren tsaron kasar Robert Gates, sun bayyana goyon bayansu ga manufofin shugaba Obama a Afghanistan, duk da matsin lamba daga majalisar dokokin kasar kan manufar yakin, da kuma adadin kudin da ake kashewa.
Mr Gates ya shaidawa manema labaru a Washington cewar, ba a baiwa sabbin manufofinsa damar su yi aiki ba.
Ya karyata rahotannin dake cewar, yakin na kubucewa gwamnatin Obama.Duk da haka ya amince cewa ba wata nasarar da za a iya bayyanawa a wannan lokaci.
Korea ta Arewa ta ce tana rukuninta na karshe, na kammala inganta makamashinta na Uranium, wanda ka iya bata damar kera bama baman nukiliya.
Tuni dai take da tashar sarrafa makamashin Plutonium.A wata wasika da ta aike ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Korea ta Arewa ta ce a shirye take ta fuskanci takunkumi, ko tattaunawa.
Wannan sanarwa ta fito ne daga kafar yada labarun kasar,alamarin da ya sa Koriya ta Kudu ta bayyana batun da cewa wata sabuwar barazana ce da ba za a iya lamunta ba.
Daren jiya ya kasance cikin kwanciyar hankali a kasar Gabon, bayan tashe tashen hankulan da suka auku, jim kadan bayan sanarwar sakamakon zaben kasar da aka yi a ranar alhamis.
Ali Bongo, 'da ga tsohon shugaban kasar Omar Bongo, shi aka bayyana da cewar ya lashe zaben, wanda ya kaiga taho mu gama tsakanin yan adawa da jamian tsaro.
Tashin hankali, ya kaiga kasashen dake makwabtaka da Gabon inda aka kona ofishin jakadancin kasar.
A jihar Agadez dake jamhuriyyar Nijar, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane uku, tare da salwantar dukiya mai yawa.
Haka kuma akalla wasu mutane dubu uku da dari biyar ne suka rasa mastugunansu, baya ga kadarori da dabbobi da kuma kayyayakin abinci da suka salwanta, ambaliayar ta kuma rutsa da makarantu da masananantu.
Ambaliyar ruwan dai ta afku ne a sanadiyyar fashewar wata korama mai suna Kori-Telwa dake dab da bakin garin na Agadez. Sai dai hukumomin Nijar sunce tuni sun soma daukar matakan shawo kan wannan matsala.
A jamhuriyar Niger wata takkaddama ce ta kunno kai tsakanin tsoffin yan majalisar dokokin kasar da hukumomin kasar. Hukumomin yan sandan Niger sun soma yiwa tsoffin yan majalisar dokokin kasar su dari da goma sha uku tambayoyi a Yamai babban birnin kasar.
Gwamnatin Kasar ce ta bukaci tsoffin yan majalisar dokokin da su bada Karin haske a game da wasu makudan kudade da hukumomin kasar ke zargin 'yan majalisar da karba ba bisa ka'ida ba tsakanin shekarun 2000 da karshen shekara 2008.
Wannan alamari na zuwa ne a daidai lokacinda, wasu rahotanni ke nuna cewar, a yau ne tsuhuwar majalisar da kawancen CFDR yayi ikirarin farfado da ita zata soma zamanta a Yamai.
Sai dai kuma Gwamnatin Nijar ta bayyana gamsuwarta game da abinda ta kira goyan bayan da taron shugabannin kasashen Afrika mambobin kungiyar AU ya baiwa shugaban kasar Malam Tanja Mammadu dangane da sauye sauyen da ya kaddamar a kasar.
Sai dai hakan yazo ne a daidai lokacin da kungiyoyin 'yan adawa da shirin tazarcen shugaban kasar, ke lasar takobin ci gaba da gwagwarmaya.
A farkon wannan mako ne dai shugabannin kasashen Afirka suka gudanar da wani babban taron kungiyar ta AU a garin Tripoli na kasar Libya, inda suka tattauna kan batun matsalolin da wadansu kasashen Nahiyar suke fuskanta da kuma duba hanyoyin magance su.
A Nigeria, wata baraka ta bullo tsakankanin 'yan jamiyyar PDP a jahar kaduna, bisa shugabancin jamiyyar a daya daga cikin kananan hukumomin jahar.
Barakar da samu ne a dalilin zaben shugabannin jamiyyar na karamar hukumar Igabi, karamar hukumar dake kunshe da wasu gaggan kusoshin gwamnati a jahar, wadanda ke adawa da juna bisa alamurranda suka shafi siyasar jahar.
An dai sami rikici yayin rantsar da shugabannin jamiyyar na karamar hukumar ta Igabi, inda matasa da dama suka hallara a wajen rantsarwar dauke da miyagun makamai aka kuma yi artabu tsakanin bangarori biyu na jamiyyar.
A yayinda wasu ke ganin an zabi sabbin shugabannin jamiyyar a bisa gaskiya da adalci, wasu kuma na zargin ba a yi adalci ba.
A Najeriyar, wasu masana harkokin tattalin arzikin sun nuna cewa sai fa Najeriyar ta yi da gaske wajen yaki da cin hanci da rashawa, wanda suka yi mata katutu.
Wannan furuci na shugabannin kungiyoyin ya zo ne, a dai dai lokacin da babban bankin kasar ya ke yin garanbawul ga harkokin bankunan a kasar. Idan dai ana iya tunawa babban bankin Najeriya ya sallami wasu manyan daraktocin bankunan biyar a sakamakon bayar da basussuka da basu dace ba.
Shugabannin jami'o'inm Najeriya sun sa baki a takaddamar dake tsakanin kungiyar malaman jami'o'i ta kasa wato ASUU da kuma gwamnatin kasar.Sai dai kuma yunkurin sulhunta bangarorin biyu bai cimma nasara ba saboda kungiyar ASSU ta ce ba zata janye yajin aikin ba.
Kungiyar ASUU dai na bukatar ganin cewa gwamnatin kasar ta rattaba hannu akan yarjjejeniyar da suka cimma domin inganta harkar koyarwa a jami'o'in kasar.
A jihar Bauchin Nigeria ana kai ruwa rana tsakanin kotun daukaka karar Shariar Musulunci da kafofin yada labarai na jiha, kan umurnin wannan kotun na dakatar da daukar duk wani rahoto daga kotunan Shariar musulunci na jihar.
Umurnin wanda shine irin sa na farko tun kaddamar da Shariar musulunci a jihar ta Bauchi a shekara ta 2001, ya haramtawa manema labarai shiga duk wata kotun Shariar musulunci domin daukar rahoto.
الجمعة، سبتمبر 04، 2009
dansudan
الاشتراك في:
تعليقات الرسالة (Atom)
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق