الخميس، ديسمبر 10، 2009

Kasar Masar na ginin katangar karfe


dansudan


Kasar Masar ta fara ginin katangar karfe a kan iyakar ta da Zirin Gaza a wani yunkuri na hana fasa-kwauri zuwa cikin yankunan kasar.


Katangar idan aka kammala za ta kai tsawon kilomita goma da kuma zurfin mitoci goma sha takwas.


Rahotanni sun ce injiniyoyin sojin Amurka ne suka tsara katangar da za'a dauki watanni goma sha takwas ana ginin ta.
Falasdinawa dai na amfani da iyakar ne wurin shigar da kayayyakin masarufi, amma Israila na zargin cewa akan yi safarar makamai da mutane ta yankin.

هناك تعليق واحد:

غير معرف يقول...

mun gode