الخميس، أبريل 14، 2011

KAMUSUN HAUSA

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Ta Jami'ar Bayero Ke Biya Hausawa


(Daga Bello Muhammad Danyaya)


Na jima ni kadai; ina ta tukuburi; ina cewa a raina; yaya malaman Hausa za su bar Hausawa cikin duhu game da sha'anin harshensu?


Sanin ma'anar kalmomin kowane harshe, shi ne mafi mahimmanci ga kowane dan harshen, da manazarci harshen, da ma bako mai sha'awar harshen.


Irin wannan abu ne ya sanya Turawa suka mayar da hankali da wuri, suka tattara kalmomin Hausa tare da fassara su cikin harshensu na Turanci, tare da buga abin, wanda muke kira kamus.


Tun a shekarar 1934 G.P. Bargery ya fitar da kamus dinsa mai suna Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary (Oxford University Press, 1934).


Bayan wannan, a cikin shekarar 1962, wani Bature mai suna R.C. Abraham, ya fito da nasa kamus, wanda ya kira Dictionary of the Hausa Language (University of London, 1962).


Wadannan kamus-kamus biyu, su ne manya, kuma kansu ne aka dogara kan neman ma'anar kowace kalma ta Hausa. Duk da yake akwai wasu kamus-kamus din, wadanda ake amfani da su, amma dai wadanda aka ambata su ne manya.


Abin kulawa a nan shi ne, duk wadannan ayuka Turawa ne suka yi su.


Abin da kuma har yanzu ba a iyar da ganewa ba, shi ne, wadannan kamus-kamus da Turawa suka yi, sun yi su ne don taimakon Turanci da Turawa, da taimaka wa Bahaushe mai sha'awar Turanci.


Babu kome! Duk da haka wadannan kamus-kamus na Turawa, sun taimaka matuka, wajen adana wa Hausawa kalmomin harshensu, har zuwa yau (2007) da Allah Ya kaddari Malaman Hausa na Jami'ar Bayero suka fito da nasu kamus wanda aka yi don Hausa da Hausawa da mai sha'awar Hausa.


Tabbas, wannan kamus na Jami'ar Bayero ya zo daidai lokacin da ake matukar bukatarsa, a lokacin da wani abu wanda aka kira “Daidaitacciyar Hausa” yake neman halakar da mafi yawan kalmomin Hausa.


Daidaitacciyar Hausa, wani salo ne da ya cilasta yin amfani da karin harshen Hausa daya, tare da zabar wasu kalmomi wadanda za a yi amfani da su a rubuce-rubuce. Inda haka ke nufin wasu kalmomin ba a yarda a yi amfani da su ba. Inda haka zai yi sanadiyar barin amfani da wasu kalmomin Hausa dangurungum. A gaba kenan kalmomin harshen Hausa za su karanta, tunda wasu kalmomin an kashe su da karfi da yaji!


Alhamdu lillahi! Wannan kamus mai suna Kamusun Hausa ya tara wadannan kalmomi na Hausa, kuma daga kowane irin karin harshe na Nijeriyar Bahaushe. Kamus din ya tara tsofaffin kalmomi, da ma sababbi. Cikin tsari kamus din ya kasance, wanda zai burge kowa.


Ko ba a so, dole a ce wa mijin iya baba. Hakika duk yawan shekarun da aka diba, wajen samar da wannan kamus, da makudan kudin da aka kashe masa, da taron dangin da aka yi masa, kwalliyar da malaman suka yi masa, ta biya kudin sabulu.


A wani gefen kuma, wannan kamus ya kashe bakin tsanya; ya rusa duk wasu gunaguni masu fitowa daga irinmu, ‘yan-ga-mu-kashe-mu na Hausa!


Ina da kira! Kiran nawa shi ne, ya zama wajibi ga jami'o'i da cibiyoyi da kwalej-kwalej masu nazarin Hausa, su yi niya su mallaki wannan kamus.


Haka ma dakunan karatu, bai kamata su yi saku-saku da wannan garabasa ba.


Kai malamin Hausa da manazarci Hausa da mai sha'awar Hausa, ina ba ku shawarar, ku yi niya ku sami naku rabo. Ina yi maku gudun wannan kamus ya kare, ya zama ba a sami damar sake buga shi ba. Ku tuna Hausawa sun ce “Fara kamun safe”.


Ga mai bukatar wannan kamus mai suna Kamusun Hausa, zai iya tuntubar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya ta Jami'ar Bayero, a ofishinta da ke harabar tsohuwar Jami'ar Bayero ta Kano. Kuma za a iya tuntubar ta, ta Jakar gidan waya. P.M.B 3011, Kano. Ko a lambar waya 060-317576, ko i-mel: csnlbuk@yahoo.com.


A cibiyar ana sayar da kwafin kamus din, a kan kudi Naira 2,000 mai makari mai kwari. Naira 1,500 mai makari mai taushi.

ليست هناك تعليقات: