Rundunar sojojin Masar ta fada jiya litinin cewa ta yarda da hakkinda ‘yan kasar suke das hi na dagewa kan bukatunsu,daga nan ta lashi takobin ba zata yi amfani da karfikan jama’a ba.
Sanarwar rundunar sojin tazo ne yayinda dubun dubatan ‘yan kasar Masar din suke ci gaba da zanga zanga a dandalin tahrir,suna ci gaba dab iris da dokar hana yawon dare a a dare na hudu,suna ci gaba da lallai lallai sai a kawo karshen mulkin shugaba Hosni Mubarak na tsawon shekaru 30.
Daga bisani sabon mataimakin shugaban kasar da aka nada ya fito a tashar talabijin ta kasar yace shugaba Hosni Mubarak ya umurce shi da ya fara tattaunawa da dukkan kungiyoyin siyasa da nufin kaddamar da sauye sauyen siyasa a kasar. Mataimakin shugaban kasa Omar Suleiman bai fayyace abinda sauye sauyen zai kunsa ba,da kuma wadanne kungiyoyi ne zai tuntuba.
Masu zanga zanga sun ayyana wata gagarumar zanga zanga a yau Talata inda mutane milyan daya zasu fita kan titunan Alkahira.
Sanarwar da rundunar sojojin kasar ta bayar bata fayyace ko ta dauki bukatar da mutane suke yi na shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus a halattacciya ba,ko dai buktar sauye sauye ne suke kallo a matsayin halattacce.
Kafofin yada labarai a Masar sun bada labarin Mr. Mubarak ya nada sabon minsitan harkokin cikin gida da kuma na kudi,a wani mataki na shawokan masu zanga zanga.Ministan harkokin waje da na tsaro garambawul da aka yi bai taba su ba.
Dubban ‘yan kasashen ketare dake kasar ne suka yi ta tururuwan barin MAsar jiya litinin. Amurka ta bada labarin ta kwashe ‘yan kasarta 1,200 da jiragen sama tara da gwamnati tayi shatarsu zuwa Turkiyya,Cyprus,da Girka a cikin sa’o’I 24 da suka wuce. Haka kuma tace tana sa ran jigilar wasu 1,400 cikin kwanaki masu zuwa
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق