الأحد، مايو 08، 2011

Takaitacan tarihin marganyi Osama Ben Ladan

An haifi Usama Bin Laden a ranar 10 ga watan Maris na shekarar 1957 a birnin Riyad na kasar Saudiya .
A 1988 ya kafa kungiyar alka’ida inda ya taimakawa dakarun neman yanci kan mamayen da kasar tarayyar Soviyat ta yiwa kasar Afghanistan.


A 1992 zuwa ta 1996 ben laden ya fara cacakar gwamnatin kasar Suadiya da ta baiwa dakarun kasar Amurka damar yin amfani da kasar ta wajen tada yakin Golf na 1990 zuwa ta 1991. Ya yi gudun hijira ya bar kasar ta saudiya.


A shekara ta 1996 bin Laden ya tare a kasar Afghanistan karkashin mulkin ‘yan taliban, a ranar 7 ga watan Ugusta na shekara ta 1998 Alka’ida ta kai hari a kan ofisoshin jakadancin amurka a Kenya da Tanzaniya inda mutane 200 suka mutu,


a ranar 11 ga watan septemba na shekara ta 2001 harin da alka’idar ta kai a kan ‘yan tawayen benayen cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya a birnin New York ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 3.


A nan take kasar Amurka ta zargi kungiya inda ta kaddamar da hari a kasar Afghanistan wanda ya haifar da faduwar gwamnatin Taliban, Ben Laden ya tsere a kasar Pakistan mai makwabtaka da Afganistan kafin ya cimma wa’adinsa a ranar 1 ga wannan wata na Mayu a garin Abbottabad (Pakistan) a karakashin harin da dakarun Amurka suka kai masa.

ليست هناك تعليقات: