dansudan
An fara wahalar man fetur a babban birnin Najeriya, AbujaAn fara wahalar man fetur a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, da ma wasu sassan kasar.
Yanzu haka dai yawancin masu ababen hawa a Abujan sun shiga tsumulmular man da suke da shi a tankunansu, ganin yadda sannu a hankali layin mai ya fara tsawo kusan a ko'ina a birnin.
Mutane kan shafe sa'o'i da dama a layin man kafin su samu biyan bukata. Wakilin BBC ya leka wani gidan mai dake unguwar Maitama, inda wasu masu motoci ke jiran tsammani a wani dogon layin mai.
Daya daga cikinsu, wanda ya ce ya kai awa biyu a layi, ya bayyana cewa, "Matsalar da ake samu [ita ce] muna bin layi sai wasu su zo su shiga.... Zuwa gobe ma sai matsalar ta wuce ta yau".
Kasuwannin Bayan Fage
Shi kuwa Isyaka Yahaya cewa ya yi wahalar man ta shafi aikinsa don kuwa "a garejinmu a yanzu haka, dole wani sa'ilin a kan dan kara kudi (ga fasinjoji) wani sa'in kuma ana aikin haka dai ba a samun wani abu".
Yayin da layukan mai ke kara tsawo a gidajen man birnin, kasuwar man ta bayan fage ta fara kankama. Wakilin BBC ya leka daya daga cikin kasuwannin bayan fagen don ganin yadda abubuwa ke gudana.
A kasuwar ta bayan fage ana sayar da lita goma sha biyu na man a kan farashin da bai kasa naira dubu da dari biyar ba.
A garejinmu a yanzu haka, dole wani sa'ilin a kan dan kara kudi (ga fasinjoji) wani sa'in kuma ana aikin haka dai ba a samun wani abu
Isyaka Yahaya
Ko da yake wahalar man ba ta sabbaba wani karin kudin mota na azo a gani ba, ta sa wasu masu ababen hawa sun fara takaita zirgazirgarsu.
Yunkurin Janye Tallafi
Ana danganta wannan karancin man ne da yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na janye tallafin da take sanyawa a bangaren man, abin da ke ci gaba da shan suka daga kungiyar kwadagon kasar da ma kungiyoyin fararen hula da dama.
Hukumar sa ido a kan farashin man fetur a kasar ta ce kawo yanzu, ba ta bada sanarwar karin kudin man ba, kuma Hukumar Kula da Albarkatun Nai ta Najeriyar (NNPC) ta ce masu shigo da man ne ke boye shi, abinda ya haddasa karancin man; da kuma rububin sayen man da jama'a ke yi saboda fargabar cewa za a kara farashi.
Dillalan man dai sun musanta zargin cewa su ne suka haddasa dogayen layuka a gidajen mai.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق