الأحد، نوفمبر 01، 2009

'Yan cin Kai A Yankin Kudancin Sudan


dansudan


Jagoran al'ummar Kudancin Sudan, Silva Kiir, ya jaddada goyon bayansa na samun 'yan cin kan yankin Kudancin Sudan.


Ana ganin wannan shine goyan baya mafi karfi kawo yanzu da Salva Kiir ya bayyana gabanin zaben raba gardamar da aka shirya yi kan makomar Sudan nan da kasa da shekaru biyu masu zuwa


Mr Kiir ya ce kada kuri'ar ci gaba da zama a matsayin kasa guda da arewacin Sudan zai mayar da 'yan kudancin kasar tamkar bayi a kasarsu.
Wakilin BBC a Sudan yace bisa dukkan alamu, furucin Mr Kiir zai kara zaman fargaba tsakanin kudanci da arewacin kasar, bayan sun shafe shekaru ashirin suna yakin basasa.

ليست هناك تعليقات: