Dan Majalisar dattijan Amurka, sanata John McCain, ya ce ya kamata a gurfanar da dan Nijeriyan nan da ake tuhuma da kokarin tarwatsa wani jirgin saman fasinja da ya doshi birnin Detroit, a kotu ta soja a matsayin mayaki na abokan gaba.
Sanata McCain ya fadawa gidan telebijin na CNN a yau lahadi cewa ba da lauya wanda zai taimakawa Umar Farouk Abdulmutallab wajen boye bayanai masu muhimmanci ya saba da ra'ayin shugaba cewar Amurka tana tsakiyar yaki da 'yan ta'adda.
Masu bin bahasin laifuffuka na tarayya sun tuhumi Abdulmutallab da laifuffuka shida, ciki har da kokarin yin amfani da makamin kare-dangi da kokarin yin kisan kai. Masu gabatar da kararraki sun yi zargin cewa saurayin dan Nijeriya yayi kokarin tayar da bam da ya boye cikin kamfansa a wannan jirgi da ya taso daga birnin Amsterdam a kasar Netherlands.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق